An nada shugaban riko na kungiyar daliban Hausa a kwalejin ilmi ta Aminu Kano hadin gwiwa da jami’ar Dustin-ma

IMG 20241226 WA1409

Sabon shugaban riko na kungiyar daliban Hausa a kwalejin ilmi ta Aminu Kano AKCOE hadin gwiwa da jami’ar tarayya da ke Dustin-ma a jihar Katsina FUDMA kuma na farko a tarihin makarantar kwamared Abubakar Sabo ya ba da tabbacin yin aiki tukuru, tare da dukkannin shugabannin kungiyar, domin samar da duk wani cigaba a tafiyar kungiyar.

Alfijir labarai ta rawaito shugaban ya nemi  hadin kan sauran wadanda suka nemi takara amma ba su sami nasara ba dama ragowar daliban makarantar na sashin Hausa, da su ba da hadin kai wajan cigaban kungiyar domin ciyar da ita gaba,  da Kuma ganin kara bunkasar harshen na Hausa a fadin Duniya.

A jawaban su daban-daban shugaban kwamitin samar da kungiyar tare tabbatuwar shugabannin rikon dakta Magaji Ahmad Gaya da sakataren sa malam Ahmad Mikha’il sun ja hankalin sabbin shugabannin rikon da su zama masu juriya da hakuri tare da gaskiya da rikon Amana don samar da cigaban kungiyar wajan ganin ta je duk in da ya kamata ta je.

An dai nada Abubakar Sabo a matsayin shugaba sai Rabi Ahmad mataimakiyar shugaba da Abdulmusawwir a matsayin magatakarda da sauran mutane goma sha biyu, a mukamai daban-daban.

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibbiyarmu ta 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *