An bukaci al’umma musammam mawadata da kuma ‘yan kungiyoyin cigaban al’umma da su dinga taimaka wadanda aka daure a gidajen a gidan ajiya da gyaran hali a fadin jihar Kano.
Bukatar hakan ta fito ne ta bakin shugabar kwamitin yiwa daurarru afuwa a jihar Kano hajiya Azumi Namadi Bebeji a zantawar ta da manema labarai. Sakamakon ban kwana da shekarar 2024.
Ta ce gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf na sane da daurarrun kasancewar akwai tanade-tanade da ya ke yi masu.
Ta kuma yabawa gwamnan da mataimakin sa, kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo bisa yadda su ke gabatar da ayyukan alheri ga al’ummar jihar.
Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibbiyarmu ta 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj