Kotun Shari’ar Muslunci ta baiwa Sheik Abdallah G/Kaya da Sheik Ibrahim Isa Makwarari Umarni

IMG 20250114 223159

Kotun Shari’ar Muslunci dake Sharada Hisba, ta umarci Sheik Abdallah G/Kaya da Sheik Ibrahim Isa Makwarari da suyi sulhu bayan shigar da kara akan zargin kafirta masu Maulidi.

A zaman kotun na wannan rana kotun karkashin mai shari’a Alkali Sani Tanimu Hausawa, tayi umarnin da duk bangarorin Shari’ar da su koma suyi sulhu domin dama tin a baya  wadanda sukai kara sunce sun rubutawa wanda ake kara takardar janye kalaman da suke zarginsa da yi, wato malam Abdallah Gadan kaya.

Daga karshe kotun ta yi umarni da a yi aiki da umarnin da ta bayar idan kuma har sulhun bai yiwu ba to idan an dawo gabatan zata yi abinda take ganin shine abinda ya dace kuma shine abinda doran Shari’a ya tabbatar, inda tace a dawo nan da makonni uku masu zuwa.

Bayan fitowa daga kotunne wakilimmu Nazifi Bala Daukawa  ya zanta da  lauyan wanda akai kara Barista kamaluddin Umar wanda yace ai dama su a shirye suke da bin wannan umarni na kotu tinda dama sun san shi sulhu alkairi ne.

Shima a nasa ɓangare Sheikh Ibrahim Isa Makwarari wanda shine ya shigar da karar yace zasu je su zauna kuma duk yadda wannan sulhun da kotu tayi umarni zasu dawo su fadawa kotu a ranar da kotu ta sanya.

Express Radio

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibbiyarmu ta 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *