Daga Aminu Bala Madobi
Wani dan bautar kasa (NYSC) mai suna Safwan Fadec ya gamu da ajalin sa a hannun wasu ‘yan bindiga a karamar hukumar Pankshin ta jihar Filato.
Fadec, wanda ke aiki a Jami’ar Ilimi ta Tarayya da ke Pankshin, Alfijir Labarai ta rawaito cewa wasu ’yan bindiga ne suka kai farmaki tare da lakada masa dukan tsiya wanda yayi sandin mutuwar sa.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Emmanuel Adesina, ya tabbatar da faruwar lamarin a hedikwatar rundunar da ke Jos A yau Talata.
Adesina ya sanar da cewa, an kama wasu maza biyu – Samuel Dang Kat da Zatshinen Wubwerwe – wadanda ake zargi da kai harin, wanda ya yi sanadin mutuwar dan bautar kasar.
A cewar Kwamishinan, an kama wadanda ake zargin ne bayan da aka gudanar da cikakken bincike tare da yin alkawarin gurfanar da wadanda suka aikata laifin a gaban kuliya.
“Wanda abin ya shafa ya yi jinya kuma Likitan da ke bakin aiki ya tabbatar da halin tsanani da yake ciki.
Daga bisani an mayar da mara lafiyar zuwa asibitin koyarwa na jami’ar Jos (JUTH) sakamakon wasu matsaloli da ya samu. Wanda daga karshe ya mutu.
“A cikin binciken da muke yi, an gano wasu mutane biyu da ake zargi, Samuel Dang Kat da Zatshinen Wubwerwe, dukkansu maza, tare da kama su kan lamarin. Ana ci gaba da kokarin damke wadanda ake zargi don gurfanar da su a gaban Kotu.”
Kwamishinan ya godewa ‘yan jihar masu bin doka da oda bisa hadin kan da suka ba jami’an tsaro wajen yaki da miyagun laifuka cikin sauki.
Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp 👇👇
https://chat.whatsapp.com/FNMJaJ3I8Sc0bkkm8aJQbQ