Gwamnatin Kano Ta Mika Ta’aziyya Ga Sarkin Kano da Shugaban APC Bisa Rasuwar  Galadiman Kano.

FB IMG 1743616610796

Daga Aminu Bala Madobi

Gwamna Abba Kabir Yusuf, a madadin gwamnatin jihar Kano da mutanen Kano ta mika sakon ta’aziyya ga mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, Majalisar Masarautar Kano dakuma Shugaban Jam’iyyar APC na Jihar Kano, Alh. Abdullahi Abbas da sauran iyalai, bisa rasuwar Galadiman Kano, Alhaji Abbas Sanusi.

Marigayi Galadiman Kano, wanda ya rasu yana da shekaru 91 a daren ranar Talata a Kano, ya kasance fitaccen dattijo kuma jigo a masarautar Kano. Ya sadaukar da rayuwarsa wajen hidimtawa Masarautar, ya rike manyan mukamai na gargajiya da suka hada da Wamban Kano, ya kuma taka muhimmiyar rawa a karkashin marigayi Sarkin Kano, Alhaji Ado Bayero.

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya bayyana wannan rashin a matsayin babban gibi, ba wai ga Masarautar kano kadai ba har ma da jihar da daukacin al’ummar Kano.

Gwamna Abba Kabiru ya yaba da kyawawan halaye na Marigayi Galadiman Kano ya bada, a matsayinsa na mutum mai hikima da tarbiyya da jajircewa wajen kiyaye al’adun Kano da al’adun gargajiya.

Gwamna Yusuf ya kara da cewa “Rasuwar Alhaji Abbas Sanusi babban rashi ne ga jihar Kano, ya kasance uba ga mutane da yawa kuma mai kula da al’adunmu masu tarin yawa, kuma za a cigaba da tunawa da hikimarsa da irin gudunmawar da ya bayar wajen ci gaban Masarautar.”

Bugu da kari, gwamnan ya jajantawa daukacin al’ummar jihar Kano, bisa babban rashi na Alhaji Abbas Sanusi. Ya yi addu’ar Allah Ta’ala ya jikansa da rahama da kuma baiwa iyalai da yan uwa ikon jure wannan babban rashi.

Gwamna Yusuf ya bukaci al’ummar Kano da su rika tunawa da marigayi Galadiman Kano a cikin addu’o’insu la’akari da irin gudunmawar da ya bada wajen cigaban masarautar kano.

Sa Hannu
Kwamaret Ibrahim A Wayya
Kwamishinan Yada Labarai Da Harkokin Cikin Gida.
02/04/2025

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan  👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *