Kwamitin wucin gadi da ke kula da lamarin Jihar Rivers ya gayyaci Kantoman riko na jihar, Vice Admiral Ibok-Ete Ibas (mai ritaya.), da ya bayyana a gabansu ranar Alhamis domin gudanar da zaman tattaunawa.
Wannan na cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Majalisar Wakilai, Akin Rotimi (Jnr), ya fitar a ranar Laraba.
Kwamitin da ke da mambobi 21, ƙarƙashin jagorancin shugaban masu rinjaye na Majalisar, Farfesa Julius Ihonvbere, an kaddamar da shi ne a ranar Talata daga Shugaban Majalisar, Abbas Tajudeen.
Majalisar Wakilai ce ta kafa kwamitin biyo bayan kudurin da Majalisar Tarayya ta amince da shi, wanda ke goyon bayan ayyana dokar ta-baci da Shugaban Ƙasa ya yi a Jihar Rivers.
A cewar Rotimi cikin sanarwar, an fitar da gayyatar ne a zaman farko da kwamitin ya gudanar a ranar Laraba, bayan kaddamarwar da Shugaban Majalisar ya yi a ranar Talata, 15 ga Afrilu, 2025.
Ya bayyana cewa zaman ya ba da damar tattauna rahotannin farko da abubuwan da ke faruwa tun bayan da kantoman ya hau mulki a Jihar Rivers.
Daily Nigerian
For more information about Alfijir labarai/Alfijir news follow here 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD