Shugaban jam’iyyar APC a Kano, Abdullahi Abbas ya yi kira ga jagoran jam’iyyar NNPP na ƙasa, Rabi’u Musa Kwankwaso da kar ya shigo APC da kungiyar siyasarsa mai suna Kwankwasiyya.
Abbas ya bayyana haka ne a wani taron manema labarai da ya gabatar a sakatariyar APC ta Kano a yau Juma’a, ya kara da cewar ba ruwan APC da wata ƙungiya ta siyasa cikin jam’iyyar.
Duk da cewa Abbas bai fadi Kwankwasiyya ba, amma a jawabin nasa ya nuna cewa babu wata kungiya ko jam’iyyar siyasa da za a bari ta shigo cikin APC.
Ya kara da cewa duk masu tururuwar dawowa APC ba za a ki karbar su ba amma sai sun je mazabu su sun yi rijista.
Ya kuma ce dukkanin shugabannin da ke rike shugabancin jam’iyyar a matakai daban-daban a jihar suna nan akan mukaman su.
” Muna sanar da duk wanda yake son shigowa APC cewa kofar mu a bude take, amma ka sani shigowar ka APC ba zai hana a EFCC da ICPC cigaba da bincikarka ba”. Inji Abdullahi Abbas
Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD