Hukumar Shari’a ta jihar Kano ta kudiri aniyar sada Al’umma da Jami’anta a Kananan Hukumomi 44

1002394726

Hukumar Shari’a ta jihar Kano tayi taron gangami da sakatarorin kananan hukumomi 44, in da aka kudiri aniyar sada Al’umma da Jami’anta a Kananan Hukumomi 44

Jawabin hakan ya fito ne ta bakin Shugaban Hukumar, Malam Abbas Abubakar Daneji a yayin daya jagoranci taro tare da Sakatarorin hukumar na Kananan Hukumomi 44.

Sheikh Daneji yace hakan da hukumar za tai zai taimaka mata wajen jin Matsalolin Al’umma da kuma Maganceta.

Shima a jawabinsa Kwamishina na 2, Sheikh Ali Danabba, yace sun gudanar da wannan taro ne ga Sakatarorin domin su inganta ayyukansu wajen wayar da kai a bangaren Shari’ar Addinin Musulunci.

A karshe Sheikh Abbas  Daneji yayi kira ga Shugabannin Kananan hukumomi da suci gaba da baiwa sakatarorin hadin kai domin inganta ayyukansu.

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news ku shiga nan  👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *