Da yake kaddamar rabon takin a karamar hukumar Madobi, gwamna Abba Kabir Yusuf yace gwamnati ta samar da takin ne domin saukakawa kananan manoma dake yankunan karkara.
Gwamnan wanda ya ce takin na hadin gwiwa ne tsakanin gwamnatin jiha da kananan hukumomi 44 ya ce kowace karamar hukuma zata samu taki tirela uku wadda ta kunshi buhu 1800 domin rabawa manoman yankinta.
Yace gwamnati zata sayarwa manoma takin akan farashi mai rahusa inda zasu samu ragin kaso hamsin cikin dari akan kowane buhu domin saukakawa kananan manoma.
Ya gargadi wadanda aka dorawa alhakin rabon takin da su kauracewa aikata almindahana KO rashin gaskiya a yayin gudanar da rabon takin inda yace gwamnati ba zata saurarawa duk wanda aka samu da hannu wajen juyar da takin ta hanyar da bata kamata ba’a.
Ya yi kira ga wadanda zasu rabauta da takin da su yi kyakkyawan amfani da Shi Yadda ya save wajen habaka nomansu domin a samu yabanya mai albarka.
Ya yabawa kamfanin samar da taki na Al-Yuma wanda ya yi kwangilar samar da takin bisa kammala aikin akan lokaci.
Yayi kira ga shugaban kamfanin da ya kara inganta kamfaninsa ta yadda kamfanin zai yi goyayya da kamfanoni na duniya.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD