Ajiyan Sokoto ya karyata jita-jitar tsayawa takarar gwamna a 2027

FB IMG 1757354750124

Ajiyan Sokoto, Alhaji Umar I. Ajiya, ya karyata jita-jitar da ake yadawa cewa yana shirin tsayawa takarar kujerar Gwamnan Jihar Sokoto a 2027.

Mai magana da yawunsa, Bashir Ahmad Danmalam,  ya bayyana jita-jitar a matsayin ƙirƙira daga wasu marasa kishin al’umma da rashin son zaman lafiya da ke son tada fitina tsakaninsa da Gwamna Dr. Ahmad Aliyu Sokoto.

Ya ce Ajiya ba shi da wani shiri na tsayawa takara, bai kuma bawa kowa izini ya buga ko ya yada posters a madadinsa ba. Ya kara da cewa Ajiya zai ci gaba da kasancewa cikakken ɗan jam’iyyar APC, tare da marawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu baya wajen ci gaban ƙasa.

Danmalam ya bukaci jama’a da su yi watsi da jita-jitar, yana mai gargadin cewa za a ɗauki matakin doka kan duk wanda ya yi yunƙurin kawo rikici ko ɓata  sunansa

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *