Hukumar Kare Hakkin Masu Amfani da Kaya ta Kasa (FCCPC) ta ce ta karbo sama da biliyan 10, kan korafin al’umma

IMG 142103 14925 1757856139176

Hukumar Kare Hakkin Masu Amfani da Kaya ta Kasa (FCCPC) ta ce ta karbo sama da naira biliyan 10 don masu amfani da kaya da suka koka a fannoni daban-daban na tattalin arzikin Najeriya.

A wata sanarwa da aka fitar a Abuja ranar Alhamis, Daraktan Hulda da Jama’a na hukumar, Ondaje Ijagwu, ya bayyana cewa an samu wadannan kudaden da aka karbo ne tsakanin watan Maris da Agusta 2025, ta hanyar tsarin karbar korafe-korafen FCCPC.

Bayanan sun nuna cewa bangaren banki ne ya fi yawan korafe-korafe da jimillar 3,173.

Sai kayayyakin masarufi masu saurin yawo (FMCG) da suka kai 1,543, kamfanonin fasahar kudi (fintech) 1,442, sannan wutar lantarki da korafe-korafe 458.

Sauran sassa sun haɗa da kasuwanci ta yanar gizo (412), sadarwa (409), dillalai da shaguna (329), sufurin jiragen sama (243), fasahar bayanai wato ayyukan kwamfuta da intanet (131), da kuma sufurin ƙasa da jigilar kaya (114).

Ijagwu ya ce korafe-korafen sun shafi matsaloli irin su cajin da ba bisa ka’ida ba, gazawar sabis, cire kudi ba tare da izini ba, tallace-tallacen yaudara, rashin fayyace sharudda, kaya marasa inganci, da jinkiri wajen magance matsaloli.

“A jimla ce, adadin korafe-korafen da aka warware a cikin wannan lokaci ya kai 9,091, yayin da kudaden da aka karbo don masu amfani suka haura naira biliyan 10.Wannan ya nuna irin girman asarar da jama’a ke fuskanta da kuma nauyin kudi da suke dauka idan babu ingantaccen tsarin kariya,” in ji sanarwar.

Hukumar ta kara da cewa rahoton ya nuna tsarin yadda jama’a ke nuna rashin gamsuwa a fannonin tattalin arziki fiye da 30, abin da ya tabbatar da bukatar karfafa tsarin kare masu amfani a Najeriya.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *