Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun! Allah ya yiwa tsohon sakataren gwamnatin Kano, Alh Sadauki Kura rasuwa

FB IMG 1757856676951

Allah ya yiwa tsohon sakataren gwamnatin Kano, Alhaji Sadauki Kura, rasuwa da safiyar yau Lahdi a asibitin Airforce da ke Kano.

Alhaji Sadauki Kura wanda ya rasu yana da shekaru 85 a duniya, ya taɓa zama manajan bankin Union Bank inda daga nan ne aka aro shi ya zo yayi sakataren gwamnatin Kano a lokacin gwamna Hamza Abdullahi.

Ya rasu ya bar matansa biyu da yaya da jikoki da dama.

Tuni aka yi jana’izar sa a gidansa da ke Gandu kusa da kwalejin Rumfa da karfe 11 na safe.

Allah ya gafarta masa ya bawa iyalansa hakurin rashinsa ameen ameen.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *