Assalamu alaikum warahmatullah wabarakatuhu mai girma Gwamna Alh Abba Kabir Yusuf Gwamnan talaka mai jin koken al’umma.
Ina yi maka addu’ar Allah ya sa a gama lafiya ameen.
Mai girma Gwamna makarantu masu zaman kansu suna cin karensu babu Babbaka! La haula lana wala ƙuwwata illa billah!
Muna roƙon Allah ya horewa iyaye abin hidimar iyali. Amma maganar gaskiya ba’a yiwa iyaye adalci. Akwai wani bincike dana gudanar akan abinda ya shafi yadda aka bar makarantu masu zaman kansu (Private schools) suke cin karensu babu babbaka.
Tabbas a waccan shekarar data gabata mai girma Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya tsawatar musu da duk iyayen da suka buƙaci a basu list din littattafai a basu, wanda yaga zai iya siya a makarantar kuma tom babu laifi.
Amma ko kun san har yanzu akwai makarantun da baka isa a baka list din littattafai ba?
Shin kun san koda an baka list ɗin wallahi akwai litattafan da baka isa ka same su ba. Zan bada misali kuma inyi ƙalubale ga wanda zai iya.
Duk makarantar da aka rubuta wadannan litattafan baka isa ka samo su ba a kasuwa
1. Quantitative reasoning na Kamfanin Rising Star
2. Verbal reasoning na Kamfanin Rising Star
3. Composition na kamfanin Rising Star
Ko kunsan me yasa ba’a samunsu a kasuwa duk yawon da zakayi? Domin su mawallafan sun hada baki da masu makarantu dayi musu alƙawarin ƙin kaiwa kasuwa wanda ya zama wajibi sai dai ka siya a wajensu kuma a farashin da suka ga dama.
Amma a gefe ɗaya akwai irin wadannan littafai na kamfanin LANTERN kuma abin mamaki sunfi wancan kamfanin chancanta ta ko wanne fanni amma saboda wasu dalilai su basa hada baki da makarantu, ana samu a kasuwa.
Zaku yadda dani idan nace muku waccan In…. daya hada kai da mutanen da suke mana wannan azaba yana da shago a …..road cikin sabon Gari zaka iya ganin littafan amma baka isa ya siyar maka ba kuma wallahi duk wanda ya iya karatu sai yaga kura-kuransa ƙarara don ina da yaƙinin baya wucewa ta gaban hukumar KERD.
Wani abin takaicin shine; a mafi yawan lokuta kuma idan an baka list din yaranka uku kuma ka same su a kasuwa to ina mai tabbatar maka zaka iya samun sassauci da bai gaza N24k ana yara ukun ba. Wannan na nuna tsabar son cin ƙazamar riba da suke da ita.
Wata masifar kuma itace yadda aka bayar da batun yin class exercise da homework cikin ‘Text books’. Yaah Rahman! Shin wannan me yake nufi? Wallahi duk salo ne na zalunci ta yadda duk abinka saika siyawa duk yaranka, wani bai isa yayi amfani da littafin dan uwansa ba wanda wannan Aminci ne. To menene amfanin exercise books? Shin dole ne sai ko wanne dalibi yana da text books kafin yayi aikin aji dana gida kenan? Iyayen da Allah bai hore musu ba yaya zasuyi?
Sai batun siyar da uniform shima. Ko kunsan har yanzu akwai makarantun da baka isa ka ɗinka uniform sa kanka ba sai dai ka siya da tsada a makarantar? Wannan fa bana maganar masu sawa kamfani suyi musu ‘customized’ uniforms. Abin takaicin kamar a uniform ilimi yake! Da yawanmu fararen uniforms muka sanya kuma Alhamdulillahi an sami abinda aka samu.
Akwai batun ‘end or term class party ko kuma ‘end of session’ ko graduation. Abin takaici wai har yaran da suka gama Nursery zuwa primary sai an tursasa iyaye wahala dinka ko hayar ‘graduation gowns’. Haka daga JSS zuwa SSS da sauransu…. Bamu san haka a makarantun gwamnati da mukayi ba ko kaɗan kuma so ake ace mana mu bamu karantu ba kenan? Isn’t this unfortunate?
Ina kira ga wanda da abin ya shafa da aiki tsoron Allah susan suna da hakki da damar takawa wannan lamari burki amma saboda wasu dalilai da ake zargi basa iya yin hakan duk da gwamnati ta basu amanar hakan.
Daga karshe wani zai iya tambayar cewa shin dole ne sai an saka yara a private bayan gana gwamnati? Amsar itace: Adadin al’ummar Kano kara faɗaɗa yake ta yadda gwamnati kaɗai ba zata iya kawar da ƙishirwar ilimi ba ita kaɗai, dole sai an kawo mata chaffa. Amma kuma itake da alhakin bibiya da tabbatar da inganci da kare muradan al’umma.
Wallahi sai Allah ya tambayi kowa bisa amanar da aka bashi daga mahukunta har iyaye…
Wasallam. Allah yasa wannan saƙon yakai ga wadanda suka chancanta. Bamu da maƙogwaro mai girman da muryarmu zata isa, amma ina fata ALLAH ya karba daga gareni aji a kuma yi gyara.
Dr. Musa Tanko Haruna (Musa Mazankwarai)
Sashin Labarin Ƙasa
Jami’ar Bayero, Kano
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t