Majalisar dokokin jihar Kano ta nemi Gwamnatin jihar ta gyara Babban Masallacin cikin Gari mai cike da tarihi.
Alfijir labarai ta rawaito a zaman majalisar jihar da aka gudanar yau, ɗan majalisar Birni, Aliyu Yusuf Daneji, ya sake kira ga gwamnati da ta gaggauta fara aikin gyaran masallaci da aka riga aka gabatar mata a baya, amma har yanzu ba a aiwatar ba.
Haka kuma, ɗan majalisar da ke wakiltar ƙaramar hukumar Rano, Ibrahim Muhammad Malami Rano, ya bukaci gwamnati ta gyara muhimman hanyoyin cikin garin Rano.
Yan majalisun biyu sun bayyana cewa gyaran masallacin da kuma hanyoyin na da matuƙar muhimmanci ga rayuwar al’umma, tare da roƙon gwamnati da ta ɗauki matakin gaggawa.
Freedom Radio
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t