Hukumar Kashe Gobara ta tabbatar da mutuwar matasa 2 da suka nutse yayin wanka a Rafin Hayin Yawa Gada, ƙaramar hukumar Tudun Wada Kano
Mai magana da yawun hukumar, ACFO Saminu Yusif Abdullahi, ya bayyana ce wa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 2 na ranar Alhamis, 9 ga Oktoba, 2025.
Ya ce ofishin hukumar da ke Tudun Wada ya samu kiran gaggawa daga jami’in Hisbah wanda ya sanar da ce wa matasan da suka nutse sun hadar da Habu Sani da Haruna Isah, dukkansu masu shekaru kusan 15.
Jami’an hukumar sun miƙa gawarwakin ga ƴansanda na sashin Tudun Wada domin gudanar da bincike.
Haka kuma, hukumar ta gano gawar wani mutum da ba’a san ko wanene ba a wata rijiya da ke Jaba Masaƙa Shago Tara a cikin birnin Kano, bayan samun rahoton kiran gaggawa daga ofishin ƴansanda na Kwalli.
Shugaban hukumar, Sani Anas, ya yi kira ga iyaye da shugabannin al’umma da su riƙa kula da ƴaƴansu tare da hana su zuwa wuraren ruwa, musamman a lokacin damina domin kare rayukansu daga irin wannan iftila’i
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t.