Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf, ya amince da wasu sabbin nade-nade tare da daga darajar wasu jami’ai, a wani yunkuri na ƙarfafa tafiyar da harkokin mulki a jihar kano.
Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin gwamnan, Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya sanya wa hannu a yau Laraba.
Waɗanda aka naɗa sun haɗa da:
1. Hon. Abdulkadir Balarabe Kankarofi (Alhajiji) – Mai Ba Gwamna Shawara na Musamman kan Harkokin Jin Kai (Special Adviser on Humanitarian Affairs), Ofishin Gwamna. Kafin wannan matsayi, Alhajiji ya riƙe muƙaminSSA Protocol I.
2. Hajiya Aisha Tamburawa – Mai Ba Gwamna Shawara ta Musamman kan Yaɗa Kyakkyawar Farfaganda (Special Adviser on Positive Propaganda). Kafin nadin, tana aiki a matsayin Supervisory Councillor a Karamar Hukumar Dawakin Kudu.
3. Engr. Mukhtar Yusuf – Darakta Janar (Managing Director), Hukumar Ayyukan Ruwa da Gine-gine ta Jihar Kano (WRECA). An ɗaga darajarsa daga muƙamin Mataimakin Darakta Janar.
4. Zakari Usman Balan – Mataimakin Darakta Janar (Deputy Managing Director), WRECA.
5. Dr. Mukhtar Bello Maisudan – Sakataren Zartarwa, Hukumar Tallafin Karatu ta Jihar Kano. Dr. Maisudan babban malami ne a Jami’ar Bayero, Kano.
Gwamnan Kano ya maye gurbin wasu daga cikin wadanda suka ajiye mukansu, ya kuma daga darajar wasu
6. Engr. Abba Kankarofi – Darakta Janar, Hukumar Gyaran Hanyoyi ta Jihar Kano (KARMA). An ɗaga darajarsa daga muƙamin Mataimakin Darakta Janar.
7. Hon. Musayyib Kawu Ungoggo – Darakta Janar, gidan zoo Kano (Kano Zoological Garden). Kafin wannan matsayi, Musayyib ya taɓa riƙe muƙamai daban-daban na siyasa da suka haɗa da kansila da Babban Mai Bayar da Rahoto ga gwamana (SSR).
Gwamna Yusuf ya yi kira ga sabbin jami’an da aka naɗa da waɗanda aka ɗaga darajarsu da su tabbatar da amincewar da aka nuna musu ta hanyar aiki tukuru, gaskiya da riƙon amana, tare da sadaukar da kai ga al’ummar Jihar Kano.
Ya jaddada cewa gwamnatinsa na ci gaba da mayar da hankali kan ƙarfafa hukumomi da aiwatar da shugabanci mai ma’ana ga jama’a, akan manufar Ajandar Kano First.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t