Ƙungiyar Lauyoyin Nijeriya (NBA) ta ce ta yanke shawarar shigar da ƙorafi ga Rundunar ’yan sandan Nijeriya da sauran hukumomin tsaro domin a binciki ikirarin da ke nuna katsalandan a harkokin shari’a.
Hakan ya biyo bayan kalaman da aka jingina wa Rabiu Musa Kwankwaso, jagoran jam’iyyar NNPP, inda ya ce a lokacin rikicin zaɓen gwamnan Kano na 2019 ya kai Abba Yusuf wurin alkalan Kotun Ƙoli bayan INEC ta ayyana zaɓen a matsayin wanda bai kammala ba.
NBA ta ce irin waɗannan ikirari na iya raunana amincewar jama’a ga ’yancin kai na bangaren shari’a da tsarin adalcin zaɓe.
Ƙungiyar ta jaddada cewa shigar da ƙorafi ba yana nufin an riga an ɗauka akwai laifi ba, sai dai domin a gudanar da cikakken bincike mai zaman kansa.
NBA ta kuma sake tabbatar da jajircewarta wajen kare bin doka da oda, da ’yancin kai da mutuncin kotunan Nijeriya.
Daily Nigerian
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t