Shugaban kasa, Bola Tinubu, ya bayar da umarnin girka sama da kyamarori 5,000 a Jihar Filato domin inganta tsaro bayan hare-haren da suka yi sanadin mutuwar mutane a Jos.
Tinubu ya bayyana hakan ne a wani taron tattaunawa da shugabannin siyasa da na gargajiya a Jos, bayan harin Palm Sunday da ya kashe fiye da mutane 27 a Angwan Rukuba.
Ya kuma umurci hafsoshin tsaro da su kamo wadanda suka aikata harin, tare da jaddada cewa dole ne a gano masu laifin.
Hakazalika, shugaban ya sanar da shirin kafa kwamitin da zai tantance asarar da wadanda abin ya shafa suka yi domin duba yiwuwar tallafa musu, yana mai cewa ko da ba za a iya mayar da rayukan da aka rasa ba, gwamnati za ta yi iya kokarinta wajen rage musu radadi.
Ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Bosun Tijani, ya ce za a yi amfani da fasahar zamani mai amfani da basirar wucin gadi (AI) wajen sarrafa kyamarorin, domin sa ido kai tsaye da kuma hanzarta daukar mataki kan barazanar tsaro.
Ya kara da cewa irin wannan tsari ya riga ya yi tasiri a wasu jihohi kamar Legas da Enugu.
Daily Nigerian
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t