Matsalar Tsaro: Amurka Ta Umarci Ma’aikata Su Fice Daga Ofishin Jakadancinta Dake Najeriya.

IMG 20260409 WA0550

Daga Aminu Bala Madobi

Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta bayar da umarni ga ma’aikatan gwamnatin Amurka dake aiki a ofishin jakadancin Najeriya dasu fice tareda Iyalan su sakamakon tabarbarewar tsaro a fadin Najeriya.

A cikin sanarwar gargadin tafiye-tafiye da ta fitar, ma’aikatar ta shawarci ‘yan Amurka da su sake nazarin yin tafiya zuwa Najeriya, saboda matsalolin aikata laifuka, ta’addanci, satar mutane da kuma rikice-rikicen cikin gida.

Sanarwar ta sanya Najeriya a mataki na 3: Na a sake tunani kafin tafiya,” yayin da wasu jihohi ke a matakin “Mataki na 4: Kada a yi tafiya kwata-kwata.”

Haka kuma, rahoton ya kara sanya jihohin Plateau, Jigawa, Kwara, Niger da Taraba cikin jerin wuraren da aka haramta tafiya zuwa gare su, wanda ya kawo jimillar jihohin da aka gargadi mutane kada su je su zuwa 23.

Sanarwar ta ce: “A ranar 8 ga Afrilu, 2026, Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ba da izinin fitar da ma’aikatan gwamnati tare da iyalansu dasu bar ofishin jakadancin Amurka da ke Abuja, sakamakon tabarbarewar tsaro.”

Jihohin da ke mataki na “4” da aka gargadi ‘yan Amurka kada su je sun hada da a Arewa: Borno, Jigawa, Kogi, Kwara, Niger, Plateau, Taraba, Yobe da arewacin Adamawa, sakamakon ta’addanci, laifuka da satar mutane. Haka kuma an ambaci jihohin Bauchi, Gombe, Kaduna, Kano, Katsina, Sokoto da Zamfara, inda aka ce ana fama da rikice-rikice, laifuka da satar mutane.

Sanarwar ta bayyana cewa tsaro a wadannan jihohi ba shi da tabbas, saboda rikice-rikicen cikin gida, tashin hankali tsakanin al’umma, da kuma laifukan da suka hada da satar mutane da fashi a kan hanyoyi. Ta kuma yi gargadin cewa ana iya gudanar da hare-haren jami’an tsaro ba tare da sanarwa ba domin dakile wadannan barazanar.

A kudanci da kudu maso gabashin Najeriya kuwa, an gargadi ‘yan Amurka da su guji jihohin Abia, Anambra, Bayelsa, Delta, Enugu, Imo da Rivers (ban da Port Harcourt), saboda yawaitar laifuka, satar mutane da rikice-rikice.

Sanarwar ta ce laifuka kamar fashi da makami, kwace motoci da kuma satar mutane domin neman kudin fansa sun yi yawa a kasar, kuma ana kallon ‘yan Amurka a matsayin masu kudi, don haka sukan zama abin hari.

Ta kuma bayyana cewa barazanar hare-haren ‘yan ta’adda na nan a fadin kasar, musamman a kasuwanni, manyan shaguna, otal-otal, wuraren ibada da tarukan jama’a.
Haka zalika, ta bayyana cewa tsarin kiwon lafiya a Najeriya yana da rauni kuma ba a iya dogaro da shi sosai, inda yawancin asibitoci ba su kai matsayin na Amurka ko Turai ba.

Ma’aikatar ta shawarci ‘yan Amurka da ke shirin zuwa Najeriya dasu tabbatar sunyi rajista a shirin Smart Traveler Enrollment Program domin samun muhimman bayanai, su yi taka-tsantsan yayin tafiya, su guji zanga-zanga da tarukan jama’a, tare da tsara hanyoyin kare kansu da tabbatar da rayuwarsu.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *