Kungiyar Tuntuba Ta Dattawan K/H Garko Ta Bukaci Jam’iyun Siyasa Da Su Tsayar Da ‘Yan Takara Da Suka Chanchanta a Kowanne Mataki Da Zasu Wakilci Garko

IMG 20260427 WA0728

Majalisar Tuntuba ta Masu Ruwa da Tsaki ta Karamar Hukumar Garko ta yi kira ga jam’iyyun siyasa da su fifita cancanta, mutunci, da kuma tarihin da aka tabbatar wajen zaɓar ‘yan takara don tsayar da su mukaman zaɓe na jiha da tarayya, a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin tabbatar da wakilci mai inganci ga al’ummar ƙaramar hukumar Garko.

An yi wannan kiran ne a lokacin wani zaman tattaunawa na masu ruwa da tsaki na manyan jami’ai da aka gudanar a Kano, inda Shugaban ƙungiyar, Hamisu Sule Garko, ya jaddada cewa zamanin tsayar da shalelen wasu mutane shugabanci ya zo ƙarshe.

Ya ce kungiyar wacce ta ƙunshi masu fasaha, masu riƙe da mukamai na gwamnati da shugabannin kasuwanci, da ma’aikatan gwamnati da suka yi ritaya, ya himmatu wajen haɓaka sabon tsarin shiga siyasa don cigaban al’umma.

“Kungiyar mu ta tuntuba ta Dattawan karamar hukumar Garko ta jaddada cewa dole a samu sauyi a yanayin da ake fitar da ‘yan takara. Muna rokon dukkan ‘jam’iyun siyasa da su tsayar da mutanen da suka cancanta don wakiltar yankinmu,” inji Hamisu Sule.

A cewarsa, kungiyar tuntuba ta al’ummar yankin, ayyukan ya ta’allaka ne akan imanin cewa ci gaba mai dorewa yana da alaƙa kai tsaye da ingancin shugabanci, yana mai ƙara da cewa Garko tana da tarin mutane masu ƙwarewa waɗanda za su iya wakiltar yankin yadda ya kamata a matakin jiha da ƙasa.

Ƙungiyar ta ƙara jaddada ƙudurinta na gano da tallafawa mutane masu halaye na gari, tana mai lura da cewa jagoranci mai inganci yana da matuƙar muhimmanci don jawo ci gaba mai ma’ana ga yankin.

> “Manufarmu ita ce mu yi tunani da kuma gano mutanen da suka tabbatar da gaskiya. Mun yi imanin cewa shugabanci mai ƙwarewa ne kawai a kowane mataki zai iya jawo ci gaban da ake buƙata ga al’ummarmu. A nan gaba, GSCC za ta yi aiki a fannoni daban-daban na jam’iyya don tabbatar da cewa Garko ba ta sake zama a baya ba, amma tana wakiltar shugabanni waɗanda suka fahimci radadi da burin mutanenta,” in ji shugaban.

Ƙungiyar ta ƙara da cewa taron ya sake jaddada alƙawarinta na bayar da shawarwari wanda ke haɓaka shugabanci mai kyau da ci gaban tattalin arziki, ba kawai a cikin Ƙaramar Hukumar Garko ba, har ma a faɗin Jihar Kano gaba ɗaya.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *