Kotu ta hana ’yan jarida ɗaukar rahoton shari’ar waɗanda ake zargi da yunƙurin juyin mulki ga Tinubu

IMG 100318 28426 1777367009872

Wata Babbar Kotun Tarayya da ke zama a Abuja, a ranar Litinin, ta umarci ’yan jarida da ke bibiyar shari’ar wasu mutum shida da ake zargi da yunƙurin juyin mulki su fice daga ɗakin kotun.

Ko da yake ba a bayyana dalilin hana zaman ’yan jaridar ba, sai dai wani jami’in kotu da bai bayyana sunansa ba ya shaida wa manema labarai cewa umarnin ya fito ne daga alƙalin kotun.

Jami’an kotu tare da hadin gwiwar jami’an tsaro na Hukumar Tsaro ta Farin Kaya (DSS) ne suka umarci ’yan jaridar su fice daga ɗakin kotun jim kaɗan kafin Mai Shari’a Abdulmalik ta shiga zaman.

Wani jami’in DSS ya ce zai yi bayani daga baya, amma har zuwa lokacin da ’yan jaridar suka bi umarnin suka fice daga kotun, bai yi ƙarin haske ba.

Wakinmu da ke kotun ya bayyana cewa ya ’yan jaridar da ke bibiyar shari’ar sun isa Kotun mai lamba 6 tun da misalin ƙarfe 8 na safe, amma aka umarce su da su fice da misalin karfe 9:10 na safe, bisa umarnin Mai Shari’a Abdulmalik.

Gwamnatin Tarayya ce ta gurfanar da mutanen shida a gaban kotu a ranar Larabar da ta gabata bisa zargin su da yunƙurin juyin mulki da bai yi nasara ba.

An ambaci sunan tsohon Gwamnan Jihar Bayelsa, Timipre Sylva, cikin zargin yunƙurin juyin mulkin, amma ba a sanya shi cikin waɗanda ake tuhuma ba, inda masu gabatar da ƙarar suka ce har yanzu ba a kama shi ba.

Waɗanda aka gurfanar da su sun haɗa da Manjo-Janar Mohammed Ibrahim Gana, mai ritaya; da Erasmus Ochegobia Victor, tsohon Kyaftin na rundunar sojin ruwa; da Sufeton ’Ya.n Sanda Ahmed Ibrahim; da Zekeri Umoru, ma’aikacin lantarki a Fadar Shugaban Ƙasa.

Sauran sun hada da Bukar Kashim Goni da Abdulkaɗir Sani, wani malamin addinin Musulunci da ke zaune a Zariya.

Ana tuhumar su da laifuka guda 13 da suka haɗa da cin amanar ƙasa, ta’addanci, ƙin bayar da bayanai da kuma wanke kuɗaɗe, amma duk sun musanta zarge-zargen.

A tuhuma ta farko, ana zargin su da shirya makirci a shekarar 2025 domin “tayar da yaƙi kan ƙasa da nufin kifar da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu,” wanda laifi da doka ta tanadi hukuncinsa a ƙarƙashin sashe na 37(2) na kundin dokokin laifuka.

Bayan gurfanar da su, kotun ta sanya ranar 27 ga Afrilu domin sauraron buƙatunsu na beli, tare da umartar a tsare su a hannun DSS.

Rahotanni na baya sun nuna cewa an kama aƙalla mutum 40 da suka haɗa da jami’an soja masu aiki da masu ritaya da kuma fararen hula dangane da wannan zargi.

Daga cikinsu, jami’an soja 36 masu aiki an gurfanar da su a gaban kotun soja a Guards Brigade Scorpion Mess da ke Asokoro, Abuja, a ranar Juma’ar da ta gabata.

Trust Radio

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *