Rundunar ‘yan sandan Najeriya ta gurfanar da wani malamin addini a Kano, Sheikh Adam Zubair Adam wanda aka fi sani da Baffa Hotoro, bisa zargin aikata laifukan yanar gizo, bata suna da kuma tunzura jama’a ta hanyar kalaman da ake zargin ya yi kan marigayi Sheikh Dahiru Usman Bauchi da kuma Sheikh Mannir Adam Koza.
Takardun karar da aka shigar a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja sun nuna cewa ana tuhumar malamin da laifuka guda shida ƙarƙashin dokar hana laifukan yanar gizo ta Cybercrimes Act ta shekarar 2015 da aka yi wa kwaskwarima a 2024.
A cewar bayanan kotun, rundunar ‘yan sanda ƙarƙashin jagorancin Sufeto Janar na kasa ce ta shigar da karar mai lamba FHC/ABJ/CR/87/2026 a ranar 10 ga watan Mayun 2026.
Lauyoyin rundunar ‘yan sandan da suka haɗa da M.K. Yahaya da R.N. Maigoro ne suka sanya hannu kan tuhumar.
Rahotanni sun ce an shirya gurfanar da Baffa Hotoro a ranar Litinin 11 ga Mayu, amma hakan bai samu ba saboda bai halarci zaman kotun ba duk da cewa an kai masa sammaci.
‘Yan sanda sun zargi malamin da amfani da shafukansa na TikTok da Facebook wajen wallafa bidiyoyi masu ɗauke da kalaman da suka haddasa ƙiyayya da tada hankali kan Sheikh Mannir Koza da marigayi Sheikh Dahiru Bauchi.
Haka kuma, bayan rasuwar Sheikh Dahiru Bauchi a watan Nuwamban 2025, ‘yan sanda sun ce Baffa Hotoro ya yi wasu kalamai masu tayar da hankali a kansa.
Masu shigar da karar sun bayyana cewa irin waɗannan kalamai na iya haddasa rikici tsakanin mabiya dariku tare da kawo barazana ga zaman lafiya.
Tun a shekarar 2023 ne jami’an DSS suka taba cafke Baffa Hotoro bayan korafin jama’a da gwamnatin Kano kan kalaman da ake zargin ya yi kan Sheikh Dahiru Bauchi.
Daga baya ya fito a wani bidiyo yana neman afuwa ga malamin da iyalansa da mabiyansa.
Sai dai bayan wasu sabbin korafe-korafe daga iyalan marigayin da Sheikh Mannir Koza, rundunar ‘yan sanda ta sake kama shi a watan Fabrairun bana kafin daga bisani a ba shi beli.
A cikin tuhume-tuhumen, an kuma zarge shi da yin kalaman da ka’iya haddasa tashin hankali tsakanin mabiyan Tijjaniyya, tare da bata sunan Sheikh Koza da marigayi Sheikh Dahiru Bauchi.
Wasu malaman addini daga bangarorin Salafiyya da Darika sun bayyana cewa shari’ar na da muhimmanci wajen rage rikice-rikicen wa’azi da kuma inganta zaman lafiya tsakanin mabiya addinai a Arewacin Najeriya.
Wani malami, Ustaz Muhammad Sagir, ya ce duk da cewa malamai na da ‘yancin yin wa’azi, bai dace a rika jingina wa Musulmi kafirci ko shirka ba ba tare da hujja ba.
Shi ma Malam Yusuf al-Maliky ya ce matakin shari’a zai taimaka wajen ƙarfafa fahimtar juna tsakanin bangarorin addini tare da rage kalaman tunzura jama’a.
Daily News 24
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t