Kotu Ta Umurci INEC Da Ta Ci Gaba Da Rijistar Masu Kada Kuri’a

Alfijr ta rawaito wata babbar kotun tarayya dake Abuja, ranar Talata, ta umurci hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa da ta gaggauta dawo da rajistar masu kada kuri’a (CVR) har zuwa kwanaki 90 kafin babban zaben 2023.

Mai shari’a Inyang Ekwo, a cikin hukuncin da ya yanke, ya kuma umurci hukumar ta INEC da ta tabbatar da cewa ba a hana ‘yan Najeriya da suka cancanta damar samun katin zabe a zabe mai zuwa ba.

Mai shari’a Ekwo ya ce alhakin da tsarin mulki ya rataya a wuyan alkalan zaben ne su samar da isassun tanadin gudanar da zaben kamar yadda dokokin Najeriya suka tanada.

“Shari’ar masu shigar da kara ta yi nasara bisa cancanta,” in ji alkalin.

Idan za ku tuna, Anajat Salmat da wasu mutane uku sun kai karar INEC a matsayin wanda ake kara a karar mai lamba: FHC/ABJ/CS/1343/2022.

A farkon sammacin da suka gabatar a gaban kotun, masu shigar da kara sun ce INEC ba za ta iya dakatar da CVR ba sabanin yadda kundin tsarin mulki ya tanada.

Sun bukaci kotun da ta umarci alkalan zaben da su ci gaba da gudanar da atisayen kamar yadda dokar kasar ta tanada.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook. Best seller Channel
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai

https://chat.whatsapp.com/Cy5n7eXK4wrHMIEYBSYpcQ

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *