Rana za ta kasance a saitin Ka’aba ranar Babbar Sallah
A ranar Laraba da misalin karfe 12:18 na rana agogon Makkah, rana za ta kasance a saitin saman dakin Ka’aba, alkiblar al’ummar Musulumi a fadin…
A karon farko cikin shekara 139, rana za ta kasance a daidai tsakiyar saman dakin Ka’aba a ranar Babbar Sallah ta bana wato Laraba 27 ga watan nan Mayu, 2026.
A ranar Laraba da misalin karfe 12:18 na rana agogon Makkah, rana za ta kasance a saitin saman dakin Ka’aba, alkiblar al’ummar Musulumi a fadin duniya.
Ana sa ran yankunan da ke wajen birnin Makkah za su yi amfani da wannan dama, a daidai lokacin domin tantance alkiblar da suke kallo wajen yin sallah.
Ranar da rana za ta kasance a daidai saman Ka’aba a karon farko cikin shekaru 139, ita ce kuma ranar alhazai ke fara yin Jifan Shaidan da yanka hadaya da kuma aski da Dawafin aikin Hajji.
Al’ummar Musulmim Mazauna gida a fadin duniya kuma a ranar, wadda ita ce 10 ga watan Zul-Hajji suke suke bukukuwan Babbar Sallah da Layya.
Kasancewar rana da daidai saman dakin Ka’aba yakan faru ne sakamakon juyawar duniya, da kuma tafiyar rana tsakanin fagen Tropic of Cancer da Tropic of Capricon.
Aminiya
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t