Alfijr ta rawaito ta rawaito Shugaban Jamhuriyar Nijar Bazoum Mohammed ya karbi tawagar ‘yan kasuwar Njjeriya da suka ziyarce shi a birnin Yammai, a karkashin jagorancin shugaban kamfanin BUA Abdusamad Isyaka Rabiu.
Da yake jawabi ga manema labarai bayan ganawar suk da shugaban kasar, Abdussamad yace sun kai ziyarar ce domin bunkasa dangantaka da kuma hadin kai tsakanin kasashen biyu.
Alfijr
Tawagar ta tattauna batutuwan da suka shafi kasuwanci da zuba jari tsakanin kasashen Nijeriya da Nijar musamman ganin irin matsalolin da duniya ke fuskanta ayau sakamakon illar da yakin ƙasar Ukraine da Rasha ya haifarwa duniya.
Shugaban kamfanin BUA wanda kuma shine shugaban kungiyar Yan kasuwan kasashen Faransa da Nijeriya yace suna shirin fadada dangantaka tsakanin kamfanin siminitin su dake Sokoto tsakanin bangarorin biyu, tare da duba wasu fannonin kasuwancin da zai shafi kasashen Nijar da Nijeriya.
Alfijr
Bua yace wannan dalilin ziyarar su da kuma ganawa da shugaba Bazoum domin yi masa bayani akan ayyukan da suke yi da kuma bukatar taimakawa juna ta hanyoyin da suka kamata.
Daga bisani shugaban kamfanin BUA ya sanar da bada tallafin Dala miliyan 3 daga gidauniyar sa dake taimakawa kasashen Afirka domin bunkasa ilimi a Nijar.