Abin Boye! Ƙungiyar Afenifere ta soki shugaban Najeriya kan fifita Yarabawa a muƙamai

Tinubu

Ƙungiyar kishin ƙabilar Yarabawa zalla ta Afenifere ta gargaɗi Shugaba Bola Ahmed Tinubu a kan abin da ta kira son kai da fifita ‘yan ƙabilar Yarabawa wajen bayar da muƙaman tarayya.

Alfijir labarai ta rawaito hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa da shugaban ƙungiyar Ayo Adebanjo, da kuma sakatarenta na yaɗa labarai Justice Faleye suka fitar a Ibadan, babban birnin jihar Oyo.

Kungiyar ta yi gargaɗin cewa lamarin zai iya zama barazana ga alaƙar ƙabilu da kuma zaman tare na lumana a tsakanin ƙabilun ƙasar.

Afeniferen ta kuma jaddada buƙatar gann shugaban ya gyara kuskuren da ta tace ya yi a kan bayar da muƙaman.

A sanarwar ƙungiyar ta ce ba za ta taɓa lamunta da tsabar son kai da nuna bambanci da Tinubu yake yi ba inda ya naɗa Yarabawa shugabannin dukkanin hukumomin yaƙi da miyagun laifuka da kuma tattalin arziƙi ba.

Afeniferen ta ce ba ta yadda za ta yi shekara da shekaru tana yaƙar abin da ta kira kaka-gida na mulkin Fulani, sannan kuma yanzu ta goyi bayan kaka-gida na Yarabawa ko wata ƙabila ba.

BBC

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibbiyarmu ta 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *