Alh Musa Jidda Ɗan Adalan Mubi Saraki ya bayyana Alhini da jimaminsa kan rasuwar dattijon arziki kuma hamshakin ɗan kasuwa Alhaji Aminu Dantata, wanda ya rasu yana da shekaru 94 a duniya.
Ɗan Adalan ya bayyana marigayin a matsayin mutum mai ƙima wanda ya taka rawar gani wajen habɓaka tattalin arziki, bunkasa ilimi, da kuma samar da ayyukan jin ƙai da zaman lafiya tare da hidimtawa al’umma da kuma kyawawan dabi’u abun koyi ga kowa a kasa da Afrika baki daya.
Ya kara da cewar Dantata mutum ne da ya sadaukar da dukiyarsa da lokacinsa wajen tallafa alumma, musamman marasa ƙarfi da su kansu masu karfin, a fadin Najeriya.
Marigayin ya bar babban gibi da zai ɗau lokaci kafin a cike shi, amma abubuwan alheri da ya gudanar a lokacin rayuwarsa za su ci gaba da haskaka tunanin al’ummar Jihar Kano da ma kasa baki daya.
Alh Musa Jidda ya miƙa ta’aziyyarsa ga iyalan marigayin, da al’ummar Jihar Kano da kuma dukkan ‘yan Najeriya dama Afrika baki daya, Allah Madaukakin Sarki da ya jikansa da rahama ya kuma baiwa danginsa haƙurin jure wannan babban rashi. Allah ya yafe masa kura-kuransa ameen ameen.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD