Akalla mutane huɗu ne aka tabbatar da rasuwarsu, ya yin da wasu 21 suka jikkata sakamakon fashewar abubuwa biyu na nakiya (IED) da ake zargin ‘yan ta’addan ISWAP ne suka dasa a karamar hukumar Gujba ta Jihar Yobe.
Fashewar farko ta faru ne da safiyar Juma’a a kan hanyar Goniri zuwa Buni Yadi, lokacin da wata mota kirar “pickup” da ke dauke da ‘yan kasuwa zuwa kasuwar mako ta Buni Yadi ta taka nakiya a kusa da kauyen Bultaram.
Fashewar ta jikkata fasinjoji da dama, inda aka tabbatar da mutuwar uku daga cikinsu bayan isar su asibitin kwararru na Jihar Yobe da ke Damaturu.
Sauran mutane 21 sun samu raunuka iri-iri kuma an kwantar da su don samun kulawa.
Leadership ta ruwaito.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD