Alhaki: An soke tashin jiragen sama fiye da 2,000 a Amurka yayin da harkokin gwamnati ke ci gaba da dagulewa

IMG 152411 091125 1762698295790

Karancin ma’aikata a cibiyoyin kula da zirga-zirgar jiragen sama na Amurka, tare da umurnin Hukumar Kula da Sufurin Sama ta Tarayyar Amurka (FAA) na rage adadin jirage da kashi huɗu a cikin 100 a manyan filayen jiragen sama 40, ya janyo soke tashi da saukar fiye da jirage 2,000 daga Juma’a zuwa Lahadi.

Ana kallon wannan soke-soken jiragen a matsayin mafi girma a sufurin jirage mafi girma a Amurka tun bayan da aka fara dakatar da gudanar da al’amuran gwamnati a ƙasar fiye da wata guda kenan.

Rage adadin jirage da FAA ta umurta ya fara da kashi huɗu a wannan karshen mako, kuma an tsara shi zai ƙaru zuwa kashi shida nan da 11 ga Nuwamba, kashi takwas nan da 13 ga Nuwamba, da kashi 10 nan da 14 ga Nuwamba.

Kamfanonin jiragen saman SkyWest, Southwest, da Envoy Air su ne kan gaba a waɗanda aka fi soke tashi da saukarsu yayin da United, Delta, da American Airlines ma suka samu jinkiri sosai, in ji FlightAware.

Kamfanonin jiragen sama dole ne su ƙara yawan raguwar jirage a hankali a cikin makon gobe, inda Sakataren Sufuri Sean Duffy ya yi gargaɗin cewa ragowar na iya kaiwa kashi 20 idan dakatarwar gwamnatin ta ci gaba.

TRT Afrika Hausa.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *