Alhazan Najeriya Da Sauran Na Duniya Sun Yi Tattaki Zuwa Dutsen Arafat A Yau Juma a

Alfijr

Alfijr ta rawaito sama da Alhazai Miliyan daya ne suka hallara a Dutsen Arafat domin gudanar da aikin Hajjin shekarar 2022, a wannan rana ta Juma a

Arafat yana daya daga cikin manyan ibadun da ake gudanar bayan an fara da kwana a Muna ranar Alhamis.

Tsayuwar Arafat bangare ne na aikin Hajji duk wanda bai samu tsayuwar ba bashi da aikin Hajjin,

Alfijr

Arfat wuri ne da Allah yake karban dukkan addu’o’in da mahajjata ke yi.

Ana sa ran mahajjata za su yi amfani da ranar yin addu’o’i ga kansu, iyalai, abokai, al’ummar musulmi da ma kasashensu.

Dutsen Arafat kuma ana kiransa da Jabal ar-Rahmah, ma’ana dutsen rahama.

A nan ne Shugaba Annabi Muhammadu Sallahu Alaihi Wasallim ya yi hudubarsa ta karshe ga musulmin da suka raka shi aikin Hajji a karshen rayuwarsa.

Alfijr

Aikin Hajjin Mahajjaci ba shi da inganci idan ba su yi la’asar ba a Dutsen Arafat.

Slide Up
x