Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Alhaji Aliko Dangote ya alƙawarta tallafa wa tsare-tsaren manunfofin taimaka wa al’umma da ci gabansu, don magance matsalolin tattalin arziki a jihar Kano.
Alfijir labarai ta rawaito Dangote ya yi wanna alƙawarin ne a lokacin da ziyarci gwamnan jihar Kano Abba Yusuf a gidan gwamnatin jihar ranar Juma’a.
Cikin wata sanarwa da sakataren yaɗa labaran gwamnan Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar ya ce Dangote ya ce yana sane da halin matsin rayuwa da talakawan ƙasar ke fuskanta.
Dangote ya alƙwarta bayar da tallafi don inganta fannonin lafiya da ilimi da hanyoyin yaƙi da talauci ga masu ƙaramin ƙarfi a jihar.
Attajirin ɗan kasuwar yayi alkawarin yin aiki kafaɗa dakafaɗa da gwamnatin jihar don bunƙasa ci gaban al’ummar jihar.
A nasa ɓangaren gwamna Abba ya gode wa hamshaƙin ɗan kasuwar bisa manyan ayyukan ci gaba da ya samar musamman sashen kula da masu buƙatar gaggawa da ɗakunan tiyata da na haihuwa da na yara a asibitin Murtala da ke jihar.
Sannan kuma gwamnan ya buƙacin Dangote ya tallafa wa jihar don gina tashar samar da wutar lantarki mai zaman kanta domin farfaɗo da masana’antun jihar don bunƙasa har tattalin arziki da kuma ƙarffa jihar.
Haka kumaAbba Kabir ya shaida wa Dangoten cewa jihar na cikin tsananin buƙatar asibitin kula da masu lalalar cutar sikila domin samar da magunguna kyauta ga masu lalurar.
A ɓangaren ababen more rayuwa, gwamnan jihar ya buƙaci tallafin Dangote don gina tituna na zamani, da gidaje, da ci gaban al’umma da sauran fannoni.
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V