Allah ya yiwa tsohuwar yar jarida Hajiya Lami Hafsat Maccido rasuwa

IMG 174140 18226 1771432913814

Fitacciyar mai gabatar da shirye-shirye a Kano, Hajiya Lami Hafsat Maccido, wadda ta kasance mace ta farko da ta fara fitowa a gidajen talabijin na NTA Kano da CTV 67, ta rasu tana da shekaru 72.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da makusancinta, Injiniya Abubakar Garba Maccido, ya tabbatar da rasuwarta, inda ya ce ta rasu ne a daren Talata bayan gajeriyar rashin lafiya.

A wata hira da ta taba yi da Muhasa Radio Kano a lokacin rayuwarta, marigayiyar ta bayyana cewa an haife ta ne a ranar 12 ga Agustan 1954 a birnin Jos na Jihar Filato. Ta ce mahaifinta Balaraben Shuwa ne daga Jihar Borno, yayin da mahaifiyarta Bafulatana ce daga Jihar Katsina.

Ta fara karatunta a Township Primary School da ke Jos, sannan ta halarci St. Louis Secondary School kafin ta wuce ABC ABU Kano domin ci gaba da karatu bayan sakandare.

Hajiya Lami Maccido ta fara aikinta a matsayin mai karbar kudi a Sheshe Departmental Stores da ke Kano, kafin ta shiga Radio Kano a shekarar 1974, inda ta yi aiki har zuwa 1976. Daga nan ta koma NTA Kano, wanda a wancan lokaci ake kira NTV Kano, inda ta yi aiki daga 1976 zuwa 1981.

Bayan haka ta koma CTV 67 a matsayin daya daga cikin ma’aikatan farko, inda ta shafe shekaru masu yawa tana hidima har zuwa ritayarta a shekarar 2012, bayan cika shekaru 35 a fannin yada labarai.

Rahotanni sun ce marigayiyar ta taka muhimmiyar rawa tare da abokan aikinta wajen sanya wa tashar suna CTV 67 a lokacin da aka kafa ta a zamanin tsohon gwamnan Kano, Abubakar Rimi.

Rasuwarta ta janyo alhini a tsakanin ’yan jarida da tsoffin abokan aikinta, wadanda suka bayyana ta a matsayin jagora kuma abar koyi a fannin yada labarai a Kano da ma kasa baki daya.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *