Wani shahararren ɗan sanda mai muƙamin Mataimakin Kwamishinan, ACP, Daniel Amah ya karɓi addinin Musulunci.
Amah, wanda yanzu sunan sa ya koma Muhammad Sanusi, ya daɗe ya na hidimtawa Musulunci a rayuwar sa.
A wani saƙo da fitaccen dan jaridar nan a Kano, Nasiru Salisu Zango ya wallafa a shafinsa na facebook, ya ce ɗan sandan har masallaci ya gina a lokacin ya na shugabancin caji-ofis na Bompai, wato DPO, a jihar Kano.
A cewar Zango, ko a lokacin yana DPO, Sanusi ya na kyautata wa masu laifi da ke tsare, inda har katifa ya saka a dakunan tsararrun don kyautata wa ga ɗan adam.
Ya kuma ƙara da cewa Sanusi mutum ne mai matuƙar kirki da taimakon al’umma kamar yadda addinin Musulunci ya koyar.

Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇
https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj