Ambaliyar Ruwan Sama Ta Tafi Da Wasu Motoci Da Mutune A Cikinsu A Jihar Lagos

Alfijr

Alfijr ta rawaito waɗanda ambaliyar ta rutsa da su, suna cikin motoci guda biyu ne a lokacin da lamarin ya faru a unguwar Oko-Oba, dake Agege jihar Lagos

Mutane uku ne ke cikin kowace mota a lokacin da ruwan ya malalo zuwa wata magudanar ruwan da ba a kammala ba tare da nutsar da motocinsu.

Alfijr

An bayyana cewa mazauna unguwar sun gargadi wadanda abin ya shafa da su daina tuki ta hanyar, amma sun jajirce suka ci gaba da tafiya har motocinsu suka nutse a cikin ruwa.

A cewar mazauna wurin da lamarin ya faru, daya daga cikin mutanen da ke cikin motar kirar Lexus jeep ya ninkaya daga cikin motar yayin da mazauna wurin suka taimaka wa sauran mutanen biyu suka fito waje.

Alfijr

Sun kuma taimakawa jami’an hukumar kashe gobara ta jihar Lagos da ke wurin domin ceto mutum na hudu.

Sai dai daya daga cikin mutanen da ke cikin motar Toyota yana ninkaya aka ceto shi, yayin da na biyun da ya yi kokarin ninkaya da na ukun da ya kasa fitowa daga cikin motar ya bace.

Alfijr

Kodinetan hukumar NEMA na yankin kudu maso yamma, Ibrahim Farinloye, ya tabbatar da cewa an ceto hudu daga cikin wadanda harin ya rutsa da su, yayin da biyu kuma ba a gansu ba.

Slide Up
x