Aminu Babba ya ci alwashin zuwa Kotun Ƙoli don ƙalubalantar hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙara kan masarautar Kano

FB IMG 1736758612626

Aminu Babba Dan’agundi, Sarkin Dawaki Babba kuma ɗaya daga cikin manyan masu naɗa sarki a masarautar Kano, ɓangaren Sarki na 15 da gwamnatin Kano ta cire, Aminu Ado Bayero, ya ce, wasa farin girki game da shari’ar masarautar Kano.

Dan’agundi ya ce zai garzaya Kotun Koli saboda bai amince da hukuncin da Kotun Ɗaukaka Ƙara ta yi ba.

Ya baiyana hakan ne a fadar Sarki ta Nassarawa a jiya  Lahadi a yayin da ya ke ganawa da manema labarai kan matakin da kotun ɗaukaka ƙara ta ɗauka a ranar Juma’a.

A tuna cewa Kotun Ɗaukaka Ƙarar ta rushe hukuncin da babbar kotu ta yi wacce ta soke dawo da Khalifa Muhammadu Sunusi II a matsayin Sarkin Kano saboda ba ta hurumin yin hakan.

Daga nan ne kotun ta ba da umarnin mayar da shari’ar zuwa babbar kotun jihar Kano wacce ke da hurumin sauraron shari’ar.

Sai dai kuma Dan’agundi ya ce sam bai gamsu da hukuncin ba, in da ya ce , “a game da shari’ar kotun ɗaukaka ƙara, kuna sane da cewa mun garzaya babbar kotun tarayya saboda batun take mana haƙƙi ne. Alƙalin ya yi amanna cewa ya na da hurumin yin hukunci game da take mana haƙƙi.

“Sun yi amfani ne da misalin shari’ar sarkin Muri wanda kotun ƙoli ta ce duk wani abu da ya shafi masarauta, babbar kotun jihar ce take da hurumi.

“Amma mu tamu ƙarar daban take da ta sarkin Muri. Amma alƙalin sai ya tafi yana wancan bayani. Sai dai ba abin da za mu yi game da hukuncin ɗaukaka ƙara, facce muma mu ɗaukaka ƙara a kan wannan hukunci.

Dan’agundi ya ce, ya bai wa lauyoyinsu umarni na su fara shirin shigar da ƙara a Kotun Ƙoli, inda ya nuna cewa su na da yaƙinin za a yi musu adalci a can.

“Tuni na bai wa lauyoyi na umarni tun a ranar Juma’ar da su samo mana kwafin waccen shari’a domin za mu ɗaukaka ƙara a kotun ƙoli. Kuma ka san ga kowacce shari’a da ta je gaban kotun ƙoli, sai dai ka yi zaman jiran sauraron hukunci na ƙarshe.”

“Don haka, ni na faɗa cewa ban gamsu da hukuncin kotun ɗaukaka ƙara ba. Na halarci zaman kotun. Shi a ra’ayinsa kamata ya yi a mai da shari’ar zuwa ga wata kotu. Ba cewa suke yi ba su yarda da mu ba. Abin da suke cewa shi ne ba su da hurumin sauraron shari’a,” in ji Ɗan’agundi.

Domin samun sauran shirye shiryenmu zaku iya biyo mu ta wannan shafukan👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *