Matasa Sun Yiwa Wani Jigo A, APC Tsirara Da Lakada Masa Duka


Alfijr ta rawaito Matasa sun yiwa wani Jigo a Jam’iyyar APC Reshen Jihar Nasarawa tsirara bayan sun lakada mishi duka a bainar jama’a.

Matasan da ake kyauatata zaton magoya bayan jam’iyyar ne sun yi wa Abubakar Abu Giza dirar mikiya ne a lokacin babban gangamin yakin neman zabe da jam’iyyar ta shirya a jihar.

Shugaban Kwamitin Shawara na Jam’iyyu IPAC a Jihar Nasarawa, Cletus Ogah Doma, ya tabbatar da faruwar lamarin, bayan an yada bidiyon abin da ya faru da Giza a Lafia, hedikwatar jihar.

Rahotanni sun bayyana cewa wannan mummunan abin ya faru da Abubakar Giza ne a Fadar Sarkin Lafia a ranar Alhamis.

Mista Ogah Doma wanda shi ne Shugaban Jam’iyyar ZP Reshen Jihar Nasarawa, ya ce babu dalilin yi wa dan siyasar tsirara a bainar jama’a, don haka ya kirayi masatan jihar da su nisanci dabanci.

Ya ce ya kamata a ce an wuce matakin irin wannan kidahumanci, sannan a matsayin matasa na kashin bayan kowace al’umma da hadin kanta, bai kamata ba su bari miyagun ’yan siyasa na amfani da su wajen aikata ba daidai ba.

Shugaban na IPAC, ya kuma yi kira ga al’ummar jihar da ma Jam’yyiar APC reshen jihar da su fito su yi Allah wadai da duk wani nau’i na dabanci da miyagun halayya da yunkurin kawo rabuwar kan al’umma.

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun Labaran mu kai tsaye

[07/12, 11:35 pm] Musa Best Seller: Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

Facebook.   Best seller Channel
YouTube.     Best Seller Channel
Twitter.        @Musabestseller
Instagram.  @musa_bestseller

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb

3 Replies to “Matasa Sun Yiwa Wani Jigo A, APC Tsirara Da Lakada Masa Duka

  1. Allah sawwakyai aidama hakan zata iya faruwa domin akoda yaushe tsanani yayi tsanani to ananne mutane sukuma suke fusata sudinga daukarwa kansu mataki Allah yasa hakan tazama izina agun Yan uwana Yan siyasa sugyara halayansu mukuma matasa yanadakyau kanfanunuwa jarida da makarantu dama gabnati suware wasu gurare nadaban Dan wayarda kan matasa akan harkar dabanci dakuma jagaliyancin siyasa bedace damuba domin mune kashin bayan al umma mune manyan gobe damune goben kasarmu zaiyikyau Allah yaza6a Mana shugabannin nagari masu sanmu da kaunarmu fiyeda yadda mumukesansu ameen.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *