Ministan Lafiya Ya Jagoranci Taron Kungiyar Mataimaka Likitocin Haƙora Na Kasa (NDTA) A Kano

IMG 122428 071125 1762514675246

Ministan lafiya ka Najeriya Prof. Muhammad Ali Pate ya bayyana yadda gwamnatin shugaba Tinubu ta mai da hankali Wajen kula da lafiyar al’umma musamman bangaren haƙora a jihohi da kananan hukumomi, musamman mutanen karkara su kara samun wayewa gurin kula da lafiyar su.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Prof. Muhammad Raji Mahmud ya bayyana a madadin ministan, don haka wannan gwamnatin ta shirya haɗaka da kungiyoyi domin kokarin wayar da al’umma birane da kauyuka domin samun wayewa wajen kula da lafiya.

Hakazalika ministan ya nemi haɗin kan yan jarida wajen wannan kokarin, in da ya bayyana babu wata Nasara da zasu iya samu ba tare da hadin kan yan jaridar ba, don haka muke muku fatan alheri

Shugaban kungiyar likitocin Masu kula da haƙora na kasa wato, Nigerian Dental Therapists Association (NDTA) Comarde FASHIM AMAYA ZETAN

ne ya bayyana cewar sun shirya wannan taro ne a jihar Kano domin kara wayar da kan al’umma duba da yadda kimiyya da fasaha suka mamaye duniya yanzu, ga kuma fasahar zamani wadda ba sai kaje ko ina ba, daga gudanka ma zaka iya kula da lafiyar haƙoranka.

Wannan dalili yasa muka zo Kano saboda tarin jama’a da ake da ita, domin mu wayar da kan al’umma su kara kulawa da lafiyar haƙoransu, don haka muka yi kokarin hadin guiwa da gwamnatin jihar Kano wajen ceto al’ummar jihar daga wannan yanayin na cututtukan haƙora.

Shima a nasa bangaren Camarde Nura Ali Sa’id shugaban kungiyar reshen jihar Kano ya bayyana cewar a kokarin su na wayar da kan al’umma dake karkara duba da yadda ake samun ciwuka daban-daban a dalilin matsalar haƙora, shi yasa muke kokarin wayar da kan su, domin kare lafiyar baki daya.

Nura ya kara da cewar gwamnatin Kano ta tanadi asibitoci guda 32 a karkara domin magance matsalolin hokora, kuma an zuba musu kayayyaki na zamani ba wai sai ka shigo gari manyan asibitoci na birni ba

Wasu daga cikin guraren da aka tanadi asibitocin sun hada da:-

Takai, Wudul, Minjibir, Rogo, Sumaila. Bebeji, Gano, Gwale, Dawakin kudu, Kumbotso, Mariri, Dambatta, Gwarzo, da sauran wurare da bamu bayyana ba.

Duk wadannan gwamnatin jihar Kano ta tanade su domin taimakawa al’umma Wajen kula da haƙoransu dai-dai da zamani.

Don haka muke kira da al’umma an kawo maaikata da kuma kayan aiki don haka zaku iya zuwa domin a duba lafiyar ku.

Dr Idris Ado Muhd wanda mataimakin Daracta ne a asibitin Malam Aminu Kano bangaren kula da haƙora ya bayyana cewar kamar ko wacce shekara da ake gabatar da wannan taron nasu, shine wannan karon muka kawo shi nan Kano, domin ba a taba yin sa ba sai wannan karon, saboda mahimmancin ta.

Dr Idris ya kara da cewar kaso 25% cikin 100 na al’ummar Najeriya basu da ilmin yadda ake kula da haƙora, don haka ake wannan taron domin wayar da kan al’umma su san yadda zasu kula da kansu saboda mahimmanci da cututtukan da suke tare da haƙora.

Don haka aka haɗa abokan aiki domin su tattauna domin zakulo hanyoyi masu sauki na zamani musamman ta hanyar AI domin kara wayar da al’umma, ko kana kan gadon ka zaka iya dubawa kasan matsalar ka da yadda zaka magance ta, kafin kazo asibiti.

Idris ya kuma yabawa gwamnatin Kano wajen samar da kayayyakin aiki da duk Najeriya babu irin su a bangaren Dental

Hajiya Binta wadda ta wakilci Gwamna Abba Kabir Yusuf ta tabbatar da goyon bayan gwamnatin Kano Wajen inganta Lafiya a jihar Kano da bada kulawa ko wace iri.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *