Alfijr ta rawaito an kama malamin Jami’a yana sace wa ɗalibai waya a Aji lokacin jarrabawa
Mutumin wanda ya ke sanye da rigar kwat da laktatyi, ya fara bin jakunan ɗalibai ɗaya bayan ɗaya yana ƙwashe wayoyinsa lokacin da suke tsaka da rubuta jarrabawa.
Sai dai hukumomi a jami’ar Obafemi Awolowo da ke Ile Ife a jihar Osun, wanda nan ne wannan lamari ya faru, sun musanta zargin cewa mutumin lakcara ne a makarantar.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun jami’ar Mr. Abiodun Olanrewaju ya fitar a ranar Laraba, ta ce, sam babu kamshin gaskiya cikin zancen.
“Eh gaskiya an kama wani mutum a aji yana sacewa ɗalibai wayoyi a jakarsu lokacin da suke tsaka da rubuta jarrabawa, amma a gaskiya wannan mutumin ba malami bane a jami’ar mu, kuma ba ɗalibi bane” inji Mista Abiodun.
“Muna zaton wani ɗan iskan gari ne ya shigo da shiga ta kamala ya aika ta wannan laifi , amma mu dai munsan ba malami ne shi a wannan jami’ar ba” inji shi
Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a
Facebook. Alfijr Labarai
YouTube. Best Seller Channel
Twitter. @Musabestseller
Instagram. @musa_bestseller
Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇
https://chat.whatsapp.com/GdLiqZyHuSz5NhjdGoGRGZ