An kama wani matashi kan yunƙurin baiwa ɗaurarru tabar wiwi a cikin burodi a Kano

FB IMG 1768463707330

Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali (NCoS), reshen jihar Kano ta bayyana cewa jami’an ta da ke aiki a gidan gyaran hali na Gwauron Dutse sun cafke wani matashi bisa yunƙurin bada tabar wiwi ga ɗaurarru a jihar

A sanarwar da Kakakin NCoS, CD Musbahu Lawan K/Nassarawa ya fitar a yau Alhamis a Kano, an kama matashin mai suna Muhammad Kabir dan unguwar Hotoro Tishama da tabar wiwi din kunshe a cikin burodi.

A cewar CSC K/Nassarawa, an kama matashin ne a harabar babbar kotun jiha yayin da ya ke yunkurin baiwa ɗaurarru wiwi bayan an kawo su kotun domin yi musu Shari’a.

Kakakin ya ce tuni dai Kwantarola na NCoS na Kano, Ado Inuwa ya bada umarnin miƙa matashin zuwa hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi, NDLEA domin zurfafa bincike da kuma gurfanar da shi a gaban kuliya.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *