An Karrama Ɗan Agaji Bayan Da Ya Tsinci Fiye Da Naira Miliyan 100 Ya Mayar

FB IMG 1709485903023

Ƙungiyar Izala ta ƙasa, JIBWIS ta karrama wani matashin ɗan agaji da ya tsinci kuɗi sama da naira miliyan 100, sannan ya mayar da su.

Alfijir labarai ta rawaito wani sako da ƙungiyar reshen jihar Bauchi ta wallafa a shafinta na Facebook, ta ce matashin ɗan agajin mai suna Salihu AbdulHadi Kankia, ya taka rawar gani, wanda ya kai a jinjina masa.

A wurin rufe taron ƙara wa juna sani na malamai masu gabatar da tafsiri, Daraktan Agaji na ƙasa Injiniya Mustapha Imam Sitti ya gabatar da matashin wanda ya tsinci jaka cike da makudan kuɗi da suka kai sama da naira miliyan 100 a Kankia da ke jihar Katsina.

”Salihu ya ɓoye kuɗin a gida, sannan ya garzaya zuwa ofishin ƴansanda ya sanar musu cewa ya tsinci jaka a yi cigiya wa al’umma amma jakar tana wurinsa”, kamar yadda sanarwar ta bayyana.

Kan wannan abin a yaba ne ƙungiyar ta Izala ta karrama matashin da lambar yabo tare da ba shi kyautar kujerar Hajjin bana.

”Sannan kuma Hon. Abdulmalik Zannan Bangudu (Ɗan Agaji kuma Dan Majalisa a Jihar Zamfara) ya bashi kyautar miliyan biyu”, kamar yadda sanarwar ta bayyana.

Sanarwar ta ƙara da cewa gwamnan Jihar Bauchi, Bala Abdulkadir Muhammed ya ba shi kyautar mota kirar bas don ya kama sana’a..

FB IMG 1709485930667
📸 JIBWIS

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijr Labarai 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H3iC9eVfJI012LJzvCQn5V

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *