An Saka Dokar Kama Duk Babur Mai Ƙafa Biyu Da Bashi Da Rijistar A Fadin Kasar Nan.

Alfijr ta rawaito hukumar Kiyaye Haɗurra ta Ƙasa, FRSC, ta umarci kwamandojin sassan 37 na faɗin ƙasar nan da su kama duk wani babur da bashi da ingantacciyar rajistar da ta dace.

Babban Kwamandan hukumar Dauda Biu ne ya ba da umarnin a wata sanarwa da jami’in yaɗa labarai, Bisi Kazeem ya fitar a Abuja ranar Litinin.

Kwamandan ya saka jaddada cewar “dukkan baburan da ba su da rajista za a kama su, ana bukatar masu baburan su kammala cikakken rajistar baburan kafin a sako su, duk babur din da aka kama, dole ne a rubuta cikakkun bayanai,’’ in ji shi.

Alfijr

Shugaban m ya ce, umarnin ya zama dole ne, biyo bayan karuwar yawan babura da ke bin hanyoyin ba bisa ka ida ba.

A cewarsa, akwai dokar ta aka tanada don kama duk baburan da basu bi doka ba, cikin kundin tsarin tantance ababen hawa na kasa, ya kuma tabbatar cewa, umarnin zai taimaka wajen dakile rashin tsaro idan duk baburan da aka kama suna cikin ma’adanar bayanai ta kasa.

Biu ya bukaci kwamandojin sassan da su gaggauta tuntubar hukumomin tattara kudaden shiga na jihohinsu, domin kafa kwamitin da zai magance lamarin.

Alfijr

Ya kuma ba da umarnin cewa, a yi hadin gwiwa da jami’an ƴan sanda da ofishin binciken ababan hawa da sauran masu ruwa da tsaki, domin tabbatar da aiwatar da dokar a fadin kasar nan baki daya.