An Yanka! Kotu Ta Yi Umarnin A Gabatar Mata Da Murja Kunya cikin munti 30 A Kano

IMG 20240213 WA0164

Babbar kotun tarayya dake zaman ta a Gyadi-gyadi dake jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin mai Shari’a Abdullahi Muhammad Liman, ta yi umarnin da a gabatar mata da Murja Ibrahim Kunya a gabanta.

Alfijir labarai ta rawaito tunda farko dai lauyoyin Murja ne suka shigar da ƙarar su, suna ƙarar hukumar Hisbah ta jihar Kano, da kwamishinan Shari’a na jahar kano, da kuma kotun shariar Muslunci ta PRP, dake jihar.

Lauyoyin Murja Kunya dai sun roki babbar kotun tarayyar ne, da a gabatar da Murja Kunya, a gaban ta, domin sun fahimci cewar anayi mu su nuƙu-nuƙu.

Idan dai ba’a manta ba tun a baya kotun ta amince da roƙon, sai dai a zaman kotun na yau lauyoyin gwamnati sun bayyana a gaban kotun ba tare da Murja ba.

Lauyoyinta sun bayyanawa kotun cewar lauyoyin gwamnati sun bijirewa umarnin kotun, sai dai kotun ta yi umarnin cewar a gabatar mata da murja cikin munti Talatin.

Rahotanni na cewa, yanzu haka Murja Kunya tana cikin kotun sakamako bin umarnin kotun da lauyoyin gwamnati suka yi.

Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *