EFCC Ta Sake Gurfanar Da Tsohon Gwamna Da Dansa Gaban Kuliya Bisa Zargin Badakalar Biliyan 29

FB IMG 1704870772714

Hukumar da ke yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta sake gurfanar da tsohon gwamna Murtala Nyako da dansa Abdulaziz a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja ranar Alhamis bisa zargin almundahanar Naira biliyan 29.

Alfijir labarai ta rawaito an sake gurfanar da su a gaban Kuliya ne bisa laifuka 37 da ake zargin sun aikata a lokacin da Mista Nyako ke gwamnan Adamawa.

Sauran wadanda aka gurfanar dasu akwai Zulkifik Abba da Abubakar Aliyu.

Kamfanonin da ake zargin sun yi amfani da su wajen karkatar da kudaden—Blue Opal Limited, Sebore Farms & Extension Limited, Pagoda Fortunes Limited, Tower Assets Management Limited, da Crust Energy Limited — sun kasance gudaa biyar zuwa na tara.

Hukumar EFCC na tuhumar Mista Nyako, da dansa, da sauran wadanda ake tuhuma bisa zargin almundahanar kudi Naira biliyan 29.

EFCC ta yi zargin cewa wadanda ake tuhumar sun karkatar da kudade daga baitul malin Adamawa tsakanin watan Janairun 2011 zuwa Disamba 2014.

 Domin Samun sauran shirye shiryenmu, Zaku iya bibiyarmu a

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Ko a latsa nan don shiga Group Whatsapp na Alfijir Labarai 👇

https://chat.whatsapp.com/CJ2q8cmhhOxFY6OEgwV5vk

Slide Up
x

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *