An Yanka Ta Tashi! Babu wata ɓaraka tsakanin Abba da Kwankwaso – In Ji Gwamnatin Kano

IMG 20241104 173819

Gwamnatin Kano ta ƙaryata zargin da ake yi kan cewa Abba Gida-Gida ya daina ɗaukar wayar uban gidansa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, inda ta ce har yanzu yana kallonsa a matsayin jagora a jam’iyya da kuma tafiyarsa ta siyasa

Alfijir labarai ta rawaito gwamnatin Kano ta yi watsi da rahotannin da ake yaɗawa kan cewa akwai rashin jituwa tsakanin Gwamnan Jihar Abba Kabir Yusuf da kuma jagoran Kwankwasiyya Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.

A ranar Litinin ne jaridar Daily Nigerian ta fitar da wani labari wanda ke zargin cewa gwamnan na Kano da daina ɗaukar wayar uban gidansa wato Rabiu Kwankwaso, lamarin da ta tayar da ƙura a kafofin sada zumunta.

Sai dai a wata sanarwa da babban mai taimaka wa gwamnan Kano kan kafofin sada zumunta Salisu Yahaya Hotoro ya fitar, ya ce babu wata rashin jituwa tsakanin Abba da mai gidan nasa Kwankwaso.

“Wannan zargin ba gaskiya bane kuma karkatar da hankali ne sakamakon Gwamna Abba yana da ladabi da alaƙa mai kyau da Rabiu Kwankwaso, inda yake kallonsa a matsayin jagora a jam’iyya da kuma tafiyarsa ta siyasa.

Duk wata magana ta ɓaraka a tsakaninsu ba wai batu ne kawai na zuzutawa ba, amma ya saɓawa mu’amularsu ta aiki,” in ji sanarwar.

“Gwamna Abba K Yusuf ya himmatu sosai wajen tabbatar da akidu da hangen nesa na jam’iyyar New Nigeria Peoples Party (NNPP). Ya himmatu wajen samar da hadin kai a cikin jam’iyyar tare da yin aiki tare da dukkan ‘ya’yan jam’iyyar ciki har da Kwankwaso domin cim ma burinmu,” kamar yadda sanarwar ta ƙara da cewa.

Domin samun sauran shirye-shiryen Alfijir labarai/Alfijir news zaku iya bibbiyarmu ta 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/ELQRQyq1zGn7zpAVP8DwNj

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *