An Yanka Ta Tashi! Matar shugaban Najeriya ta zare hannunta kan maganar addu’ar zaman lafiya ta ƙasa da za ayi

Mrs Tinubu

Uwargidan Shugaban Kasa Oluremi Tinubu ta musanta hannunta a wata addu’a ta kasa da aka ce za a yi domin rokon Allah kan mawuyacin hali da kasar ke ciki.

Alfijir labarai ta rawaito wata majiya tace Uwargidan Shugaban Kasa da mai bada Shawara kan harkokin tsaro na Kasa (NSA), Malam Nuhu Ribadu, suna cikin wani shirin addu’a na kwana bakwai kan halin da kasar ke ciki.

A cewar wani rahoto da aka danganta da Darakta Janar na Kungiyar Addu’a Ta Kasa, Segun Afolorunikan, an ce matar Tinubu da Ribadu suna cikin masu shirya shirin da aka kira ‘Neman Shiga Tsakanin Allah a Lamurran Najeriya.’

Rahoton ya ce Afolorunikan ya bayyana cewa za a gudanar da wannan shiri tare da hadin gwiwar manyan malaman addinan Kirista da Musulmi.

Sai dai mai magana da yawun Uwargidan Shugaban Kasa, Busola Kukoyi, ta karyata wannan labari a cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Asabar.

Ta ce, “Wannan shi ne don fayyace wa jama’a cewa Uwargidan Shugaban Kasa, Sanata Oluremi Tinubu, ba ta shirya wata addu’a ta kasa ba.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *