BBC ta ruwaito cewa an sace ɗan sandan mai suna CSP Ibrahim Aliyu Ishaq wanda shi ne DPO na ofishin yan sanda da ke Fugar, a kan hanyar Auchi zuwa Agenebode a jihar Edo.
CSP Ishaq kafin komawarsa jihar Edo yayi aiki a ofishin ƴan sanda da ke Dakata a jihar Kano.
Rahotanni sun tabbatar da Cewar a bana dai an kai hare-hare ga ofisoshin yan sandan Najeriya da dama musamman a kudancin Najeriya inda aka ƙona Chaji office a ƙwace makamansu.
Allah ya dawwamar mana da zaman lafiya a wannan kasar tamu baki daya ameen.