Farfesa Gwarzo ya taya FUDMA murna yayin da take gudanar da taron hadaka.
Shugaban Jami’ar Maryam Abacha American University (MAAUN) da Franco-British International University (FBIU), Farfesa Adamu Abubakar Gwarzo ya taya jami’ar tarayya ta Dutsinma (FUDMA) murnar samun nasara karo na 5, da taro karo na 6 da aka yi a ranar 27 ga watan Nuwamba, 2021 a harabar jami’ar Dutsin-Ma, jihar Katsina.
Masanin ilimin kasa da kasa, Farfesa Gwarzo, wanda kuma shi ne Shugaban Kungiyar Jami’o’in Masu Zaman Kansu (AAPU) daga baya ya kaddamar da hanyar da Hukumar Gudanarwar Jami’ar Tarayya ta Dutsin-Ma ta gina tare da sanya masa suna bisa la’akari da jajircewarsa na yin amfani da wannan hanya wajen tallafawa da inganta ilimi a yankin kudu da hamadar sahara.
Shugaban MAAUN ya samu rakiyar wata tawaga mai karfi da suka hada da shugaban makarantar koyon karatun digiri na biyu, Farfesa Sunusi Magaji Rano, daraktan hulda da hadin gwiwa, Dr. Bala Muhammad Tukur, shugaban makarantar kimiyyar na’ura mai kwakwalwa, Mataimakin Farfesa Ibrahim Lawal. Dokta Habib Awais, Babban Malami a Sashen Turanci da Harsunan Turai, Dokta Abdullahi Garba, Babban Malami, Tsangayar Nazarin Zamantakewar Jama’a, Dakta Musa Jibia, Babban Malami, Shugaban Harkokin Dalibai.
Allah ya kara mana irin su Ferfesa Adamu Gwarzo a Arewacin kasar nan tamu ameen.