An ɗage jana’izar marigayi Alhaji Aminu Ɗantata saboda wasu dalilai

FB IMG 1751105495315

Gwamnatin Najeriya ta sanar da ɗage jana’izar fitaccen ɗankasuwar nan, Alhaji Aminu Dantata da ya rasu ranar Asabar a ƙasar Hadaɗɗiyar Daular Larabawa.

Ministan yaɗa labaran Najeriya, Mohammed Idris ya tabbatar wa da BBC ɗage jana’izar sakamakon rashin isar gawar marigayin a kan lokaci zuwa birnin Madina.

”Akwai ƙa’idoji da gwamnatin Saudiyya ta shimfiɗa kan yadda za a shigar da gawa domin yi mata jana’iza a ƙasar, to yanzu haka ana nan ana ta cike-ciken takardu tsakanin gwamnatin Saudiyya da iyalan mamacin,”in ji ministan.

Mohammed Idris ya ce idan an kammala za a ɗauko gawar daga Hadaɗɗiyar Daular Larabawa zuwa Saudiyya.

Ya ƙara da cewa tuni ofishin jakadancin Najeriya a Saudiyya da iyalan mamacin suka kammala shirye-shiryen jana’izar.

Bayanai sun ce Alhaji Aminu Ɗantata ne ya bar wasiyyar binne shi a birnin Madina, inda kuma ƴan’uwansa suka nemi amincewar hukumomin Saudiyya game da buƙatar, suka kuma amince da ita.

Tun da safiyar yau ne tawagogin gwamnatin tarayya da na gwamnatin jihar Kano suka tafi Saudiyyar da nufin halartar jana’izar da aka shiryi yi a yau Litinin.

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/KoLt2IMlnQfJPP6zNrcNKD

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *