Ana Wata! An Ƙara Kuɗin Fasfo A Najeriya

FB IMG 1756386520993

Hukumar kula da Shige da Fice ta Najeriya (NIS) ta sanar da cewa daga ranar 1 ga watan Satumba, 2025, za a ƙara kuɗin yin fasfo na ƙasar.

A cikin wata sanarwa da kakakin hukumar, ACI AS Akinlabi, ya fitar a ranar Alhamis, ya ce ƙarin zai shafi masu neman fasfo a Najeriya ne kawai.

Sanarwar ta bayyana cewa fasfo mai shafi 32 zai koma N100,000, yayin da na shafi 64, wanda zai yi shekara goma kafin ƙarewa, zai koma N200,000.

Sai dai kuɗin da ’yan Najeriya mazauna ƙasashen waje ke biya bai canza ba – ana ci gaba da cajin Dala 150 ga fasfo mai shafi 32 da Dala 230 ga na shafi 64.

Hukumar ta ce wannan ƙarin kuɗin na cikin shirin da aka ɗauka don ƙara inganci da tsaron fasfo, tare da tabbatar da cewa ya ci gaba da samuwa ga ’yan ƙasa.
Domin neman Karin bayani ko saka muku talla sai a tura mana Sakon Whatsapp ta wannan lambar

Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835

Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇

https://twitter.com/Musabestseller?s=09

https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165

https://www.threads.net/@alfijirlabarai

https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12

https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag

Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇

https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *