Gwamnan Jihar Rivers, Siminalayi Fubara, ya sanar da janyewarsa daga zaben fidda gwani na kujerar gwamna na jam’iyyar APC da aka shirya gudanarwa ranar Alhamis.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, a cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu da kansa a daren Laraba, Fubara ya ce ya dauki matakin ne bayan dogon nazari da tuntuba da iyalansa da makusantansa.
Ya bayyana cewa zai mara wa duk wanda ya fito takarar jam’iyyar baya domin tabbatar da hadin kai da zaman lafiya a jihar.
Fubara ya ce shugabanci yana bukatar sadaukarwa, yana mai cewa akwai lokacin da buri na kai dole ya ba muradun jama’a gaba.
“Jihar Rivers ta fi karfin kowane mutum guda, kuma a wannan lokaci mai muhimmanci, zaman lafiya, kwanciyar hankali da hadin kan jihar su ne ya kamata su fi kowanne buri muhimmanci,” in ji shi.
Ya kuma gode wa magoya bayansa bisa goyon bayan da suka ba shi tun daga farkon tafiyar siyasarsa, duk da cewa ya fahimci takaicin da wasu daga cikinsu za su iya ji bayan janyewar tasa.
Fubara ya ce shiru da ya yi a baya-bayan nan ya kasance ne bisa dabarar siyasa da kuma kare muradun jihar.
Har ila yau, ya gode wa jam’iyyar APC bisa damar da ta ba shi tare da nuna godiya ga Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu, kan goyon baya da karfafa masa gwiwa.
Gwamnan ya jaddada cewa janyewarsa daga takarar ba alamar tsoro ko gazawa ba ce, illa sadaukarwa domin tabbatar da ci gaban jihar Rivers cikin hadin kai da zaman lafiya.
Ya kuma tabbatar da cewa zai ci gaba da yi wa al’ummar jihar Rivers hidima har zuwa karshen wa’adinsa.
Ga masu son bada talla ko shawarwari a kira wannan lambar +2348032077835
Domin samun sauran shirye-shirye Alfijir labarai/Alfijir news ku biyo mu ta nan 👇
https://twitter.com/Musabestseller?s=09
https://www.facebook.com/profile.php?id=100089640289165
https://www.threads.net/@alfijirlabarai
https://www.youtube.com/@BestsellerChannel12
https://www.instagram.com/musa_bestseller?utm_source=qr&r=nametag
Alfijir labarai Alfijir News Whatsapp Group 👇👇
https://chat.whatsapp.com/H5oBRaZBdCVIyOTIV5eMfb?mode=ac_t